التين

At-Tin

Sura ta 95 · ta Makka · ayoyi 8 · Tsarin saukarwa: 28

Rubutu
Fassarori

Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
  1. Abubakar Mahmoud GumiInã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa Dũr Sĩnĩna.
  1. Abubakar Mahmoud GumiDa wannan gari amintacce.
  1. Abubakar Mahmoud GumiLalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiSa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
  1. Abubakar Mahmoud GumiFace waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
  1. Abubakar Mahmoud GumiTo, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
  1. Abubakar Mahmoud GumiAshe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?