العلق
Al-'Alaq
Rubutu
Fassarori
Taɓa kalmar Larabci don ganin karatunta, tsarinta da tushenta.
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
- Abubakar Mahmoud GumiKa yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
- Abubakar Mahmoud GumiYa hahitta mutum daga gudan jini.
- Abubakar Mahmoud GumiKa yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
- Abubakar Mahmoud GumiWanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
- Abubakar Mahmoud GumiYa sanar da mutum abin da bai sani ba.
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
- Abubakar Mahmoud GumiDõmin yã ga kansa, yã wadãta.
- Abubakar Mahmoud GumiLalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
- Abubakar Mahmoud GumiShin, kã ga wanda ke hana.
- Abubakar Mahmoud GumiBãwã idan yã yi salla?
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
- Abubakar Mahmoud GumiKo ya yi umurni da taƙawa?
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
- Abubakar Mahmoud GumiAshe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
- Abubakar Mahmoud GumiMakwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
- Abubakar Mahmoud GumiSai ya kirayi ƙungiyarsa.
- Abubakar Mahmoud GumiZã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
- Abubakar Mahmoud GumiA'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).